Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
- Indexed episodes, last 90 days
- 11
- Latest publication
- Sep 21, 2026
- Audience
- Checking…
- Earliest in this view
- Jul 6, 2026
Latest episodes
Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta (opens the original)
Read excerpt
Bisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a Najeriya duk shekara-Rahoto (opens the original)
Read excerpt
Shirin Lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar dajin mahaifa da ke addabar mata musamman a Nahiyar Afrika. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.
Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba (opens the original)
Read excerpt
Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, musamman a ɓangaren cutukan da suka shafi zazzabin cizon sauro da ciwon kai da kuma tari baya ga ciwon
Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma (opens the original)
Read excerpt
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa. Ku danna almar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna (opens the original)
Read excerpt
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Publishing over time
Last 90 days. Choose a month to open its work.
Recurring subjects
Named in the text we hold. One piece can cover several.
Audience
No verified audience measurement yet.
About this data
Counts cover the work we have indexed. Tone needs enough text and a confident classification. Excerpts and episode notes are not full articles or transcripts.
Identity or attribution wrong? Suggest a correction.